Thursday 1 January 2026 - 21:35
Dole ne Itikafi ya Kasance na Jama'a Kuma Ya Zama Cibiyar Zurfafa Ilimi ga Matasa

Hauza/ Shugaban makarantun addini (Hauza) na ƙasar Iran, ya jaddada muhimmancin kiyaye yanayin i'itikafi a matsayin wani yunkuri na jama'a (ba na gwamnati kawai ba). Ya bayyana wannan ibada a matsayin wata dama mai mahimmanci wajen zurfafa ilimin addini, kare tunani, da tarbiyyar matasa daga hare-haren tunani da na al'adu. Ya kuma jaddada bukatar yin tsari na bai daya, samar da hanyoyin samun kudin shiga masu dorewa, da karfafa hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin Hauza don bunkasa wannan harka ta ruhi.

A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, shugaban makarantun addini (Hauza) na kasar Iran, ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da mambobin babban kwamitin shirya i'itikafi. Ya bayyana i'itikafi a matsayin "fitila mai haske da kuma tushen kusanci ga Allah." Ya kara da cewa: "Muna fatan itikafin bana ma, kamar na shekarun baya, ya zama sanadiyyar shiriya, daukakar ruhi, da kuma sanya matasa amfana sosai daga kusanci ga Allah. Kuma dukkanmu mu kasance daga cikin bayin Allah na kwarai masu hidima ga ibada."

Ya bayyana cewa yin hidima a tafarkin i'itikafi wani babban nauyi ne na Ubangiji da ya rataya a wuyan kowa, inda ya ce: "Wannan tafarki ne na godiya ga Allah; don haka muna mika godiya ga wannan rukuni na malamai da dukkan masu hidimar i'itikafi a fadin kasar wadanda suke kokari cikin soyayya da sha'awa domin gudanar da wannan taro na ruhi cikin daukaka. Muna gani a sassa daban-daban na kasar yadda mutane ke tsaye da soyayya da kauna ga masallaci, ibada, da ambaton Allah."

Jaddada Muhimmancin Kasancewar I'itikafi na Jama'a

Shugaban makarantun addini (Hauza) na ƙasar, yayin da yake ishara da bayanan da mambobin babban kwamitin i'itikafi suka gabatar, ya bayyana cewa: "Kamar yadda nake faɗa a kowace shekara, akwai wasu muhimman maki a wannan tafarki. Abu na farko shi ne kiyaye kasancewar itikafi a matsayin harka ta jama'a. Wannan yunkuri dole ne ya kasance na mutane ne gaba ɗaya; na mutane nagari, masu kishin addini, da muminai. Dole ne i'itikafi ya ci gaba da kasancewa gaba daya na mutane. Duk inda bukatar hakan ta taso domin kare yanayin jama'a na wannan yunkuri da kuma kiyaye dokokinsa na ruhi da na ma'ana, tare da kasancewar manyan masana addini da al'ada, a shirye nake in yi hidima kuma na ɗauki hakan a matsayin wajibi a kaina."

Ya ce: "Ayyukan i'itikafi dole ne su dogara ga gudunmawar jama'a. Babu matsala idan aka samu taimakon mutane na lokaci-lokaci ko ma gudunmawa don samar da hanyoyin samun kuɗi masu dorewa, amma asalin aikin dole ne ya kasance na mutane ne, kuma ina jaddada wannan batu sosai."

Sannan Ayatullah A'arafi ya kawo magana kan batu na biyu, wato bukatar tsari da hangen nesa a cikin gudanar da i'itikafi, inda ya ce: "Duk wani aiki da ake son ya samu bunƙasa da ci gaba mai dorewa, yana bukatar ka'ida, tsari, takardar shiri (document), hangen nesa, nazarin gaba, bincike, da kuma tsare-tsare; tabbas tare da kiyaye asalin sa na kasancewa na jama'a. Cikin farin ciki, kun ɗauki matakai masu kyau da wannan ra'ayi, kuma ya zama dole a ƙarfafa wannan tsarin fiye da kowane lokaci."

Mamba a babban kwamitin gudanarwa na makarantun addini (Hauza), ya bayyana batu na uku a matsayin kokarin samar da hanyoyin samun kudi masu dorewa domin i'itikafi, inda ya ce: "Idan har za ku iya tsara wasu samfura kamar Waqafi da sauran hanyoyin kudi masu dorewa domin samar da tallafi na din-din-din ga i'itikafi, to wannan aiki ne mai kyau kwarai. Ko da ana bukatar wasu tallafi domin samar da wadannan hanyoyi, ni a shirye nake in taimaka. Ya kamata a tsara wani tsari mai sauki wanda ya dace da yanayin i'itikafi, wanda zai iya daukar nauyin wannan harka ta ruhi na dogon lokaci."

Yayin da yake jaddada sarkakiyar yanayin tunani na matasan wannan zamani, ya kara da cewa: "Matasan yau suna fuskantar farmakin bayanai da ra'ayoyi daga dubban hanyoyi daban-daban.

Wani bangare na wannan yanayi ya samo asali ne daga sauye-sauyen duniya, wani bangaren kuma saboda an sanya kasarmu a gaba ne a cikin wani yaki na musamman domin raunana tushen tunani da fahimtar al'umma. Saboda haka, matasan da suke karkata zuwa ga itikafi suna da kima sosai, kuma ya kamata a san darajarsu."

Ayatullah A'arafi ya fayyace cewa: "Wadannan matasa ya kamata a zurfafa musu ilimi da tabbatar musu da akida, sannan a tarbiyye su a matsayin masu yada al'adu da sakon ruhi; ta yadda su da kansu za su koma dakarun kare darajoji na Ubangiji da kuma harkar i'itikafi. Wannan yana bukatar tsari na musamman, da zakulo hazikai a tsakanin masu i'itikafin, da kuma samar musu da hanyoyin yin tasiri a cikin al'umma. Tare da haka, dole ne a iya isar da sakon i'itikafi a hankali ga wadanda ba su riga sun shiga wannan tafarki ba; wannan aiki ne mai wahala da yake bukatar tunani, fasaha, da tsari."

Ya ci gaba da cewa: "A wasu fannonin, ba mu iya ba wa wannan tsara (na matasa) cikakkun amsoshin da suke bukata ba. Wani sashe na matsalolin ya samo asali ne daga yanayin tattalin arziki da zamantakewa, wani sashen kuma ya danganci fasahar mu, fahimtarmu, da iyawarmu. Duk da wahalhalu, bai kamata mu bar fagen fama ba; sai dai mu tsaya mu ci gaba da aiki. I'itikafi yana da tasiri sosai a wannan tafarki, domin yana tattare da nishadin ibada da kuma yanayi na gwagwarmaya, wanda zai iya kawar da cikas na tunani da na ruhi."

Shugaban makarantun addini na kasa ya jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi a fannin itikafi, inda ya ce: "A shekarun baya-bayan nan, an samar da wata hanyar sadarwa ta bai daya (network) mai kunshe da mutane dubu ashirin zuwa talatin, wanda ya kamata a yi amfani da su sosai wajen hidimar i'itikafi. Ya zama dole a karfafa alakar akalla sassa goma sha biyar na makarantun Hauza da wannan harka ta ruhi, kuma kowane sashe ya ayyana takamaiman ayyukansa a fannin bincike, wa'azi, amsa shubuhohi, nazarin dabaru, ilimi, da kuma ayyukan kasa da kasa."

Yayin da yake ishara da nasarar da aka samu wajen hadin gwiwar hukumomin wa'azi a lokacin tura malamai na watan Ramadan, ya bayyana cewa: "A watan Ramadan da ya gabata, an tura malamai kusan dubu 45 cikin cikakken hadin gwiwa tsakanin hukumomi da dama, ba tare da wani sabani ba kuma cikin hadin kai. Ya kamata a bi wannan tsari a fannin i'itikafi ma. Ya zama dole a tsara cikakken jerin ayyuka, shugabanni, da lokutan gudanarwa domin karfafa alaka tsakanin hukumomi kamar Hukumar Yada Addinin Musulunci , Ofishin Yada Addinin Musulunci, Jami'atul Mustafa, Cibiyar Hidima ta Hauza, Hauzar Mata, da kuma Jami'atuz Zahra (SA)."

Ayatullah A'arafi ya kuma jaddada ba da muhimmanci na musamman ga bangaren i'itikafi na kasa da kasa, inda ya bukaci a tsara wani shiri mai zaman kansa na musamman a wannan fanni tare da hadin gwiwar Jami'atul Mustafa.

A karshe ya kara da cewa: "Game da bangaren mata kuma, la'akari da nauyin da ya rataya a wuyanmu da manufofin da ake da su, ya kamata a yi tsari mai kyau tare da ba da tallafin da ya dace, musamman ga watan Ramadan, koda kuwa ana cikin yanayi na karancin kasafi."

A ƙarshe, Shugaban makarantun addini na ƙasar ya jaddada muhimmancin samun sakamako na gaske daga tarurrukan da ake yi, da kuma tsara wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin hukumar gudanarwar Hauza da kuma kwamitin haɗin gwiwa na sauran hukumomi. Ya bayyana cewa: "Sakamakon waɗannan haɗin gwiwar dole ne ya haifar da tsare-tsare na aikace-aikace a ƙasa. Abin da yake da muhimmanci shi ne aiki, kuma tabbatar da waɗannan manufofi zai yiwu ne kawai ta hanyar jajircewa, ikhlasi, da ƙoƙarin bai ɗaya."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha